http://ricqyultra.com/2018/10/26/bulala-undisputed/

Intro

Nan gani, nan bari

Kayan kamfani daban da na shago

A bakin tsoho ne goro kan tsufa

A bari ya huce shi kan kawo rabon wani

A rashin kira karen bebe ya bata

A so uwa, a so yayan ta

Haaa (RICQY ULTRA SAYssss)

 

VERSE #1

Daya, Biyu, 1, 2 bishiya, na gaji da yin turanci kai

I want to drink za kwana

(yace wai zai sha kwana)

Baturan nan wai tambaya yake

Ya sunan danwake da English

Sai nace masa son of a beans

Sai yace nine “son of a bitch”

Kai jan kosai tsaya ka ji

Turanci ba dole bane

A kasar hausa an san mu da tarbiya, ga hankali, ga kirki

 

CHORUS

Idan ka zage ni zan zazane ka da bulala

Har ga Allah ba wasa, gafara I’m the undisputed

Idan ka zage ni zan fyafyade ka da baitoci

Har ga Allah ba wasa, gafara I’m the undisputed

 

VERSE #2

Jamma’a wai suna mamaki wai ya za a ce na iya Hausa

Da na leko sai suka koma

(Har ma wai rapping yake yi da Hausa)

Wai shin ya zaku yi da ni

Wai kun zo ne dan ku bincike i?

Albishirin ki, ba’ayi wa kujeran sarki gori

Sai ni kujera, ku zo to ku zauna

Duk wani sarki yana da lokacin sa

Amma kujeran sarki zamanin sa baya karewa

 

CHORUS

Idan ka zage ni zan zazane ka da bulala

Har ga Allah ba wasa, gafara I’m the undisputed

Idan ka zage ni zan fyafyade ka da baitoci

Har ga Allah ba wasa, gafara I’m the undisputed

 

VERSE #3

Wai ga haters suna mazurai

Muna a daki, suna a soro

Hausa hip-hop ta muku nisa

Ga yan tsaki suna ta tsoro

Mune zakarun gwajin dafi

A gan mu,a ji mu, dole a bar mu

Hausa hiphop ta muku nisa

Na zama miyau, dole a hadiye ni

Idan zaka ja da zabin Allah, sai ta kai ka ga hallaka

Addu’ar mu itace makami

Tana rusau toh rugu-rugu, kaca-kaca

 

CHORUS

Idan ka zage ni zan zazane ka da bulala

Har ga Allah ba wasa, gafara I’m the undisputed

Idan ka zage ni zan fyafyade ka da baitoci

Har ga Allah ba wasa, gafara I’m the undisputed

REPEAT 2X

OUTRO

Duk abun da za kayi, kayi don Allah

Allah raba mu da mahasada

Idan kana da shi, za ayi Magana

Idan baka da shi za ayi Magana

Amma shiru ma amsa ne

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *